Yansanda Sun Kama Riƙaƙƙun Masu Laifuka Su 7 a Katsina
Tuesday, 02 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

‘Yansanda Sun Kama Riƙaƙƙun Masu Laifuka Su 7 a Katsina

 

Rundunar 'yansanda a Katsina sun kama wasu gungun yan fashi da makami da suka ƙware wajen ɓalle shaguna da ƙwacen wayar hannu a cikin birnin Katsina.

 

Mai Magana da yawun rundunar 'Yansanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu, shi ne ya fitar da sanarwar haka, inda ya ce dukkan su suna zaune a layin Ɗan Haƙo da ke unguwar shararrar pipe cikin garin Katsina.

 

A cewar sa, waɗanda suka sun haɗa da Abubakar Dayyabu mai shekara 19 da aka fi sani da Antu,sai Abdulrahaman Danjuma mai shekara 25 da ake kira Aguero da Dahiru Nuhu mai shekara 21 da ake kira Tsoho.

 

Sauran sun haɗa da Muhammad Yahaya mai shekaru 21 da ake kira Lucas da Bello Balele mai shekaru 34 da shima ake kira Na Ande.

 

Sai Abubakar Idris mai shekaru 20 da ake kira Makale da Shafi’u Lawal Ɗan Fefe.

 

DSP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa, 'yan sanda sun kama mutanen ne a maɓoyan su a Shararrar Pipe bayan samun labarin fasa babban shagon kayan masarufi a bayan babbar kasuwar Katsina.

 

Ya ce, bincike da suka gudanar, an samu adduna guda biyu, wuƙaƙe guda biyu da dogon ƙarfe a maɓoyan su.

 

Sadiq ya ƙara da cewa, da zarar 'yansanda sun gama bincike za a gurfanar da mutanen a gaban kotu.

 

Tunda farko, Kwamishinan 'Yansanda CP Bello Shehu, ya tabbatar wa al’ummar jihar musamman a garin Katsina cewa rundunar za ta cigaba da tabbatar da kare rayukan al’umma da dukiyar su.

 

Ya nemi gudunmawar al’ummar jihar na bada bayanai na sirri kan maɓoyan miyagun mutane a jihar.

 

Ya kuma yaba da jami’an sa kan ƙwarewa da jajircewa da suke nunawa wajen gudanar da aikin su na samar da wanzuwar zaman lafiya.