Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Muhammad Sani Bello ya ce ba wanda aka kama zuwa yanzu dangane da harin da aka kai wa ayarin motocin tsohon Ministan Shari’a na Nijeriya, Abubakar Malami, amma ana ci gaba bincike, duk da cewa 'yan sandan na zargin 'yan dabar siyasa ne suka kai harin.