Kwamishinan ya kuma bayar da umarnin a miƙa wannan shari’a zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha da ke Birnin Kebbi, domin gudanar da cikakken bincike da nufin cafke sauran mambobin kungiyar da suka tsere da kuma kwato dukkan dabbobin da aka sace.
CP Bello M. Sani ya jaddada cewa rundunar ‘yan sanda ta himmatu matuƙa wajen yaki da laifukan tashin hankali domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.
Ya kuma roƙi al’ummar jihar Kebbi da su kasance masu lura da halin da ake ciki tare da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci ga ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro domin samun gaggawar ɗaukar mataki.

CSP Nafiu Abubakar, anipr
Jami’in Hulɗa da Jama’a,
Don Kwamishinan ‘Yan Sanda,
Hedikwatar ‘Yan Sanda, Jihar Kebbi
2 ga Satumba, 2025.