Ba batun jiran karɓar umurni; Shugaban Rundunar Tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya kara jaddada wa sojojin Nijeriya cewa, sun san babban aikin da aka ɗauke su shi ne kare rayukan al'umma
Don haka, ba tare da bata lokaci ba, duk wani makiyin da suka ga yana neman rayuwarsu ko ta abokan aikinsu, su harbe shi
Haka kuma ya ce duk wani makiyin da ke kokarin kai hari wurin da suke tsaro, ko al'ummar da suke ba kariya, shi ma wannan doka ta ba su damar su harbe shi, ba tare da wani jira ko jinkiri ba, kin yin hakan kuma za su iya gurfana a gaban Kotun sojoji