Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda.
Thursday, 04 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Duk budurwar da ta ci kuɗin saurayi kuma ta ƙi zuwa wajensa ta karya doka – ’Yan sanda.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta yi gargadin cewa sabon salon da ’yan mata suka fito da shi na karbar kudin samarinsu da nufin za su je wajensu amma su ki zuwa laifi ne da za a iya hukunta su da shi.

A cikin wani bidiyo da Kakakin rundunar a jihar, Grace Iringe-Koko, ta wallafa ranar Laraba, ta ce yin hakan daidai yake da da damfara, kuma za a iya hukunta duk wacce ta aikata.

A cewar kakakin, “Me ya sa za ki karbi kudi daga wajen mutum kuma ki ki zuwa wajensa, hakan laifi ne da mai aikata shi zai iya fuskantar hukunci.