YAN SANDA SUN KAMA MASU FASA-KWABO NA BABURA HUDU, DA MASU KARBAR KAYAN SATA BIYU, SUN KWATO BABURA UKU A KALGO
Rundunar 'yan sandan Jihar Kebbi ta ci gaba da ƙoƙari don gano hanyoyin da wannan ƙungiya ke bi da kuma kama sauran membobinta.
A ƙoƙarinta na kawar da dukkan nau’ikan laifuka daga Jihar Kebbi, Rundunar 'Yan Sandan ta samu wani muhimmin nasara a yaƙi da fasa-kwabon babura a jihar.
A cikin watan Agusta 2025, wani Aminu Umar (namiji) daga Al’amin Villa Kalgo, ya kai ƙara a hedikwatar ‘yan sanda ta Kalgo, inda ya bayyana zargin cewa mutanen nan:
1. Tirmizi Tukur
2. Abubakar Lauwali
3. Mudassiru Danbala
4. Ibrahim Sani
duk maza, sun haɗu ne suka sace masa babur ɗinsa na Haijue (baki), wanda bai da rajista.
Bisa sahihan bayanan sirri, rundunar ‘yan sanda a Kalgo ta kai samame a wani wuri da ake zargi da zama maboyar masu laifi, inda suka kama waɗanda ake zargi. A yayin wannan samame, an gano babura guda biyu, duka jajaye ne, kuma ba su da rajista (Bajaj). A yayin bincike, masu laifin sun amsa cewa sun sace baburan ne daga ƙauyen Kajiji, a karamar hukumar Tambuwal, Jihar Sakkwato.
Haka kuma, an kama wasu mutane biyu da ake zargin suna karɓar kayayyakin sata, su ne: