Tsaron Sokoto Tsaro: Matasa a jihar Sokoto sun sha alwashin kare kansu saboda "sakacin gwamnati"
Thursday, 04 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Tsaro: Matasa a jihar Sokoto sun sha alwashin kare kansu saboda "sakacin gwamnati"

Matasa a karkashin kungiyar Shagari Youths a karamar hukumar Shagari ta jihar Sokoto sun yi barazanar daukar matakin kare kansu sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin.

Matasan sun kuma zargi gwamnati da sakaci duk da hare-haren ’yan bindiga da ake ta fama da su tare da korafe-korafen jama’a.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a madadin kungiyar ta hannun Bello Bala Shagari, ya bayyana cewa matasan sun yanke wannan shawara ne a wani taro na yanar gizo da suka gudanar ranar Laraba.

Ya ce: “Da dama sun bayyana cewa gwamnati ta gaza wajen cika alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Saboda haka, kare kai yanzu shi ne kadai zaɓin da ya rage.”

Ya kara da cewa matasan sun yanke shawarar daukar duk wani mataki da ya dace domin kare kansu daga cin zarafi da hare-haren ’yan bindiga.

Sai dai  Shagari ya bayyana cewa dan majalisar tarayya mai wakiltar Yabo/Shagari, Umar Yusuf-Yabo, ya yi kira da a yi hakuri, a bi doka, tare da samun karin shawarwari.

Duk da ya nuna fahimtar takaicin da matasan ke ciki, ya roki gwamnati da ta hanzarta daukar mataki domin dakile abin da ya ce na iya “rikidewa zuwa barazana mai girma.”

“Matasan sun gaji da jira kuma suna rasa kwarin gwiwa ga hukuma. Tura jami’an tsaro cikin gaggawa zuwa Shagari zai sake tabbatar da kwarin gwiwar al’umma tare da hana tashin hankali.

“Idan gwamnati za ta amince da tsarin kare kai cikin tsari, matasan Shagari a shirye suke su samu horo yadda ya kamata domin kare kansu da iyalansu a karkashin doka,” in ji sanarwar.