Mutane da dama sun mutu bayan rushewar sama da gidaje 500 daga jiya zuwa yau a Batsari jihar Katsina
Daga daren jiya zuwa wayewar safiyar yau Juma’a, rahotanni sun tabbatar da cewa akalla gidaje sama da 500 ne suka rushe a ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, sakamakon mamakon ruwan sama da aka tafka.
Wannan mummunan hali ya haifar da dimbin asarar dukiya, inda dubban gidaje suka rushe tun daga farkon damina har zuwa yanzu.
Baya ga asarar gidaje, an ruwaito cewa wasu daga cikin mazauna yankin sun rasa rayukansu, yayin da wasu kuma suka samu raunuka daban-daban sakamakon iftila'in.
Wannan lamari ya ƙara tayar da hankulan jama’a, musamman mazauna yankin da ke rayuwa cikin damuwa da rashin tabbacin matsuguni.
Sahel24 Tv ta ruwaito cewa, al’umma da dama sun yi kira ga gwamnati da hukumomin agaji da su gaggauta kai ɗauki, tare da tallafawa waɗanda abin ya shafa.
A halin yanzu, mutane da dama na addu’a Allah Ya kawo saukin wannan ruwan sama da ke haddasa rushewar gidaje a yankin, tare da bada ikon gyara da dawo da gidajen da aka rasa.