Matsalar yunwa Matsalar yunwar ta fi ƙamari ne a Arewa-maso-Gabashin ƙasar, inda aka yi ƙiyasin cewa iyalai miliyan 2.3 suka tarwatse a cikin shekara 16 na rikicin Boko Haram.
Saturday, 06 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 31 ne ke fuskantar ƙarancin abinci a Najeriya, wanda hakan ne mafi yawa a tarihi, sanadiyyar rage kudin tallafi da Amurka da sauran ƙasashen Yamma ke bayarwa.
 
Matsalar yunwar ta fi ƙamari ne a Arewa-maso-Gabashin ƙasar, inda aka yi ƙiyasin cewa iyalai miliyan 2.3 suka tarwatse a cikin shekara 16 na rikicin Boko Haram.
 
A baya, Amurka ce take bayar da kashi 60 cikin ɗari na tallafin jin-ƙai a Najeriya; sai dai, shugaba Donald Trump ya dakatar da tallafin. A yanzu, ƙasashen Yamma sun mayar da hankali wajen kashe kuɗi kan tsaro sanadiyyar barazana daga Rasha.
 
A sanadiyyar haka, ala tilas Najeriya ta zabtare kuɗin da take kasaftawa na tallafin jin-ƙai daga dala miliyan 910 zuwa dala miliyan 300.
 
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce rikici, sauyin yanayi da matsin tattalin arziƙi da ambaliyar ruwa sun ƙara munana matsalar ƙarancin abinci.