Wasu fusattatun matasa sun farmaki mataimakin gwamnan jihar Sokoto saboda hare-haren yan bindiga. A kalla an kama mutum hudu bayan hari kan tawagar mataimakin gwamnan Sokoto da yake dawowa daga ziyarar jaje a Shagari.
Jami'an tsaro sun dauki mataki kan wasu da ake zargin sun farmaki mataimakin gwamnan jihar Sokoto Wasu fusatattun matasa ne suka kai hari kan tawagar mataimakin gwamnan a karamar hukumar Shagari Rahotanni sun ce wasu da bala’in ‘yan bindiga ya raba su da muhallansu ne suka tare hanya, suka kai hari kan tawagarsa.