Kuɗin da ake baiwa jihohi ya ninka tun bayan cire tallafin man fetur – Gwamnatin Tarayya
Saturday, 06 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kuɗin da ake baiwa jihohi ya ninka tun bayan cire tallafin man fetur – Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce kuɗaɗen da ake baiwa jihohi sun ninka tun bayan da aka cire tallafin man fetur a watan Mayun 2023.

Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arzikin Ƙasa, Wale Edun, ne ya bayyana haka yayin taron tattaunawa kan kuɗaɗen kiwon lafiya da aka gudanar a Abuja.

“A cikin shekaru biyu da suka gabata, sauye-sauyen da aka yi sun zo da ƙalubale, amma sun taimaka wajen gyara tattalin arzikin da ya lalace.” inji shi

Ya kara da cewa, “Cire tallafin man fetur ya kasance babban mataki mai wahala, amma ya dawo da daidaiton kuɗi ba wai ga Gwamnatin Tarayya kaɗai ba, har ma da jihohi. Jihohi yanzu na samun ninki biyu daga abin da suke karɓa a da.”

Edun ya bayyana cewa tallafin man fetur ya kasance “wani tarkace da ba ya amfanar Talakawa, sai ƴan kaɗan da wasu ƙasashen waje, kuma yana cinye kusan kashi 2.5% na GDP na ƙasar.”

Ya ƙara da cewa cire tallafin ya ba da dama ga gwamnati ta karkata kuɗaɗe zuwa muhimman fannoni kamar kiwon lafiya da ilimi, duk da cewa:

“Za a ɗauki lokaci kafin a farfaɗo daga dogon rashin saka hannun jari a waɗannan sassa.”

Tun bayan cire tallafin, farashin litar man fetur ya tashi sama da Naira 1,000 a wasu wurare, sai daga baya ya sauka ƙasa da Naira 900.

Sai dai kuma, duk da cewa al’ummar ƙasa na ci gaba da koke kan tsadar rayuwa, gwamnatin tarayya ta ce alamar sassaucin tattalin arziki ta fara bayyana.

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce adadin hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa kashi 21.88 cikin ɗari a watan Yuli, daga kashi 22.22 cikin ɗari a watan Yuni. Wannan na zuwa bayan hauhawar da ta kai kashi 27 cikin ɗari a bara, mafi girma cikin shekaru da dama.

Farashin kayan abinci kuwa ya tsaya a kashi 22.74 cikin ɗari a watan Yuli na bana, idan aka kwatanta da kashi 39.53 cikin ɗari a shekarar da ta gabata.