Rikicin Shugabanci Ya Kunno Kai a PDP: Gwamnonin PDP na Neman Shekarau, Yazama Shugaban Jam'iyyar Tawagar Wike na Ƙoƙarin Naɗa Ortom
Wani sabon rikici ya sake bayyana a jam’iyyar PDP, yayin da gwamnonin jam’iyyar da kuma magoya bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, suka shiga takaddama kan muƙaman jagoranci a matakin ƙasa.
Bincike ya nuna cewa gwamnonin PDP na ƙoƙarin tabbatar da tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin sabon Jam'iyyar na Ƙasa . A gefe guda kuwa, tawagar Wike ta dage wajen ganin tsohon Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom, ya hau wannan kujerar.
Masu sharhi sun bayyana cewa wannan rikicin zai iya ƙara raba kan manyan jiga-jigan jam’iyyar idan ba a samu yarjejeniya cikin gaggawa ba. Duk da haka, har yanzu shugabannin jam’iyyar ba su fito da matsayinsu na ƙarshe ba, lamarin da ya sa jama’a ke cigaba da sa ido kan yadda za a kammala wannan rikicin shugabanci.