Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya,
Sunday, 07 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Mayaƙan Boko Haram sun kashe aƙalla mutum 55 a arewa maso gabashin Najeriya, a wani hari da suka kai kan wasu mutane da suka koma garinsu daga sansanin ƴan gudun hijira, a jiya Asabar.
 
Harin ya auku ne a daren ranar Juma'a, a garin Darul-Jama a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno, garin da ke tsakanin Najeriya da Kamaru.
 
Wata majiya ta shaida wa  ƴan jaroda cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin guda 55, har da sojoji guda biyar, da kuma wani ɗan sa-kai guda ɗaya.
 
Mazauna yankin sun ce mayaƙan sun ƙaddamar musu da harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, inda suka ce maharan sun kutsa garin ne a kan babura ɗauke da muggan makamai, inda suka fara harbe-harben kan mai-uwa-da-wabi, sannan suka riƙa ƙone gidaje.