A yau, na samu gagarumar girmamawa na karɓar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, a gidana. Ziyarsa ta kasance alamar goyon baya da jajantawa a wannan lokaci da nake fama da illar farmakin da wasu ‘yan daba da ake zargin jam’iyyar APC ta ɗauka suka kai mini a Jihar Kebbi.
Na yi matuƙar jin daɗi da wannan ziyarar tasa, inda tattaunawarmu ta jaddada bukatar gaggawa ta ganin ‘yan Najeriya – ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka ke bi ba – sun tsaya tsayin daka wajen kare zaman lafiya, tsaro, da kuma bin doka da oda. Wannan ya tuna mana cewa demokuraɗiyya ba ta ginu akan firgita mutane ko tashin hankali ba, sai dai akan tattaunawa, gaskiya, da mutunta juna.
Ina nan daram bisa jajircewata na ganin an samu adalci da kare ‘yancin al’umma. Abin da ya faru a Jihar Kebbi wani gargaɗi ne da ya kamata a ɗauka da muhimmanci – game da amfani da tashin hankali don cimma muradun siyasa da kuma yunƙurin dagula tsarin demokuraɗiyya ta hanyar barazana. Irin waɗannan abubuwa ya kamata a la’anta su kuma a hukunta su daidai da doka.
Har ila yau, wannan hari da aka kai mini ba shi ne na farko ba. Kwanaki kaɗan da suka gabata, wasu ‘yan daba da ake zargin suna aiki da jam’iyya mai mulki sun kai hari a wani taron haɗin gwiwar ADC a Kaduna wanda Mallam Nasir El-Rufai ya jagoranta. Manyan shugabannin jam’iyyar da suka halarci taron sun ji rauni, an lalata motocin su, duk da kasancewar jami’an tsaro a wurin.
A haka ma, a Lagos, an kai wa Gbadebo Rhodes-Vivour – tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Labour – hari a lokacin gangamin jam’iyyar adawa a Alimosho. Wadanda suka halarci gangamin sun ji rauni yayin da ‘yan daba da aka ce an ɗauko su suka tarwatsa taron.
Wadannan hare-hare da suka faru a jere a jihohi daban-daban alamar ne da ke nuna irin haɗarin da ke tattare da tsarin siyasar tashin hankali da ake ƙoƙarin amfani da shi don hana masu adawa yin ayyukansu cikin ‘yanci.
Ina miƙa godiya ta musamman ga Alhaji Atiku Abubakar bisa wannan ziyarar tasa ta lokaci da kuma kwarin gwiwar da ya bani. Wannan ya nuna cewa shugabanci na gari na nufin fifita ƙa’ida da gaskiya fiye da siyasa, da kuma nuna cewa abubuwan da muke da su a haɗe da ƙasa da demokuraɗiyya su fi ƙima fiye da banbancin jam’iyya.
Bari wannan lokaci ya zama kiran tashi gare mu duka: hanyar gina Najeriya mai ƙarfi tana cikin haɗin kai, adalci, da kuma tsayawa akan gaskiya ba tare da jin tsoro ba.