Kwamishinan 'yan sandan jihar Kebbi a arewacin Najeriya ya ce wasu mutane biyu sun shiga komarsu bayan kamasu da cin-zarafin wasu yara biyu 'yan shekaru biyar da 10.  
Thursday, 11 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kebbi a arewacin Najeriya ya ce wasu mutane biyu sun shiga komarsu bayan kamasu da cin-zarafin wasu yara biyu 'yan shekaru biyar da 10.  

Rundunar ta ce an ci-zarafin yaran ne lokacin da aka aiki guda shago sayen alawa, yayin da dayar kuma makwabcinsu ne ya kai ta dakinsa ya ci-zarafinta.

'Yan sanda na Kebbi sun ce lamarin fyade na kara ta’azzara a tsakanin al’umma, yana mai kira ga gwamnati ta dauki tsauraran matakai