Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a satar zinare da kimar sa ta kai Naira miliyan 109
Thursday, 11 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a satar zinare da kimar sa ta kai Naira miliyan 109.5 a garin Ka’oje, karamar hukumar Bagudo.

Mai magana da yawun rundunar, Nafiu Abubakar, ya ce an shigar da korafi ranar 4 ga Satumban 2025 a sashen bincike na SCID, Birnin Kebbi, wanda ya kai ga gano cewa wani jami’in hukumar gyaran hali, Ibrahim Abubakar ne ya saci kayan.

Rahoton ya ce Abubakar ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa ya sayar da kayan ga wasu dillalai daga Sokoto da Kebbi, ciki har da Sa’adu Ibrahim Darhami, Hamza Ahmad, Nasiru Sani, da Tasi’u Umar.

Bincike ya kuma nuna cewa wani Ibrahim Usman Oroji ya taimaka wajen rarraba kayan, inda ya karɓi naira miliyan 2.5 a matsayin rabonsa.