Kantoman Rivers Ibas ya Bayyana Kammala Aikin da Tinubu ya ba shi na Gwamnan Rikon Kwarya
Saturday, 13 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kantoman Rivers Ibas ya Bayyana Kammala Aikin da Tinubu ya ba shi na Gwamnan Rikon Kwarya 

Kantoman Ribas Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas mai ritaya ya bayyana cewa ya kammala sauke nauyin da shugaban Najeriya ya dora masa na daidaita dimukuradiyya a jihar.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal, yayin da yake gabatar da rahoton zaben kananan hukumomin jihar da ya gudana.

Kantoman ya ce sauke nauyin da ke kansa ya kammala ne bayan gudanar da zabuka a tsaftace tare da rantsar da shugabannin kananan hukumomin da suka yi nasara, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.