Yan Bindiga Sun Saki Ma'aurata da Ɗiyarsu a Katsina Bayan Biyan Naira Miliyan 50 Kuɗin Fansa
Thursday, 18 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Yan Bindiga Sun Saki Ma'aurata da Ɗiyarsu a Katsina Bayan Biyan Naira Miliyan 50 Kuɗin Fansa

'Yan bindiga sun sako matashin Ɗan kasuwa, Anas Ahmadu, tare da matarsa Halimatu mai juna biyu na wata bakwai, da kuma ‘yar su ‘yar shekara biyu, da aka yi garkuwa da su cikin garin Katsina. 

Rahotanni sun tabbatar da cewa an sako su ne da daren Laraba, bayan shafe kwanaki 21 a hannun masu garkuwa.

Wani daga cikin ‘yan uwa na kusa, wanda bai so a bayyana sunansa ba, ya shaida cewa an biya kudin fansa na Naira Miliyan 50 kafin a sako su.