Kotu ta yanke wa wani sojan Najeriya hukuncin k!sa ta hanyar rataya
Thursday, 18 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kotu ta yanke wa wani sojan Najeriya hukuncin k!sa ta hanyar rataya 

Rahotanni na nuna cewa wata kotun soja ta musamman (General Court Martial) da ke Maxwell Khobe Cantonment, Jos ta yanke wa Private Lukman Musa hukuncin k!sa ta hanyar rataya bayan ta same shi da laifin kas!he Abdulrahman Isa a garin Azere, Jihar Bauchi. 

Majiyar Ayau News ta ruwaito Kotun ta tabbatar da cewa akwai gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifinsa, inda ta yanke masa hukuncin k!sa bisa ga dokar sojojin Najeriya.