Kungiyar likitocin zuciya ta Najeriya, (NCS) ta nuna damuwarta yadda cutar hawan-jini ke ci gaba da yaɗuwa a ƙasar, inda ta ke gargadin cewa kashi 40% na mutane na dauke da cutar a Najeriya.
Friday, 19 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kungiyar likitocin zuciya ta Najeriya (NCS) ta nuna damuwarta yadda cutar hawan-jini ke ci gaba da yaɗuwa a ƙasar, inda ta ke gargadin cewa kashi 40% na mutane na dauke da cutar a Najeriya.
 
Kungiyar ta bayyana haka ne a taro ‘Karo na Hamsin-da-huɗu’, wanda take yi duk shekara domin tattauna hanyoyin inganta lafiyar zuciya.
 
An gudanar da taron ne tare da taron 17th Biennial Pan African Society of Cardiology (PASCAR) a ƙarƙashin taken: “Hanyoyin rage farashin cutar cututtukan dake kama zuciya a Afrika”.
 
Da yake bada jawabinsa a wurin taron, tsohon shugaban kungiyar NCS, Okechukwu Ogah ya ce hawan-jini na daga cikin manyan cututtukan dake wa Gwamnatin Najeriya barazana.