Shugaba Tinubu ya kai ziyara gidan tsohon Shugaban Ƙasa Buhari da ke Kaduna, Inda ya Gana da Iyalansa.
Ziyarar ta kasance cikin girmamawa da kuma jajantawa dangin tsohon shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, tare da jaddada irin gudunmawar da Buhari ya bayar wajen gina ƙasa.
An rawaito cewa Shugaba Tinubu ya yaba da kyakkyawan irin gudummawar siyasa da shugabanci da marigayi Buhari ya bayar ga Najeriya, tare da tabbatar da cewa gwamnati ba za ta manta da tarihin sa ba.
Hotunan wannan ziyara sun nuna Shugaba Tinubu tare da manyan iyalan marigayi Buhari suna musayar gaisuwa da ta’aziyya.