
NNPP Ta Nesanta Kanta Da Shirin Kwankwaso Na Shiga APC
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta bayyana cewa shirin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na komawa jam’iyyar APC ba na jam’iyyar NNPP bane, illa kawai nasa ne da mambobin Kwankwasiyya Movement.
Sakataren Ƙasa na jam’iyyar, Dr. Ogini Olaposi, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Legas a ranar Litinin.
A Ranar Asabar, Kwankwaso wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a zaɓen 2023, ya sanar da cewa shi da magoya bayansa sun shirya tsaf don shiga jam’iyyar APC mai mulki. Sai dai ya yi gargaɗi cewa ba za su amince a yi amfani da su wajen cin zaɓe a watsar da su ba daga baya.
Da yake mayar da martani kan wannan batu, Dr. Olaposi ya ce sanarwar da Kwankwaso ya yi ta tabbatar da cewa shi da motsin Kwankwasiyya ba su da alaƙa da NNPP.
“A ƙarshe, Gaskiya ta bayyana. Duk wata tattaunawa da za a yi da Kwankwaso daga kowace jam’iyya ya zama kawai a matsayin nasa na mutum, ba tare da jam’iyyarmu ba,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan mataki ya tabbatar da da’awar jam’iyyar cewa Kwankwaso da magoya bayansa sun rabu da NNPP tun bayan korarsu bisa zargin gudanar da ayyukan cin amanar jam’iyya.