Wata sabuwar cutar fata ta jefa al’ummar ƙauyen Malabu cikin fargaba a Jihar Adamawa, inda ta yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu 67 suka kamu da ita.
Monday, 22 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Wata sabuwar cutar fata ta jefa al’ummar ƙauyen Malabu cikin fargaba a Jihar Adamawa, inda ta yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da wasu 67 suka kamu da ita.
 
Jami’an Lafiya na Gwamnatin Tarayya sun fara gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin cutar. Kodinetan riƙo na shirin kula da cutukan tarin fuka, fata da sanyi mai tsanani, Dakta Adesigbin Olufemi, ya tabbatar da al’amarin a wata hira da manema labarai a jiya Lahadi.
 
A cewarsa, tun daga ranar 10 ga watan Satumba, an samu tabbacin mutane 68 sun kamu da cutar, inda takwas daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali a Asibitin Koyarwa na Modibbo Adama, Yola.
 
Cutar, wadda ke haifar da ƙuraje masu fashewa da lalata fata da ƙasusuwa, ta jefa al’ummar Malabu cikin tashin hankali.
 
Binciken farko ya nuna cewa cutar ta samo asali ne daga Gambon Fatar Jiki wato Buruli Ulcer, wadda aka fi samun ta a yankunan ruwa.
 
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce gano cutar da wuri na taimakawa wajen rage yaduwa da haɗarin mutuwar mutane.