Hukumar DSS ta Gayyaci Abubakar Malami SAN domin Amsa Tambayoyi.
Monday, 22 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Hukumar DSS ta Gayyaci Abubakar Malami SAN domin Amsa Tambayoyi.

Tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami (SAN), ya tabbatar da cewa Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyace shi domin yi masa tambayoyi kan binciken harin da aka kai masa da tawagarsa a Jihar Kebbi ranar 1 ga Satumba, 2025.

Malami ya bayyana cewa binciken na DSS yana da nasaba da wata korafi da wasu fitattun ‘yan siyasa na jihar suka shigar.

Ya kuma yaba wa DSS bisa yadda take gudanar da binciken cikin kwarewa da gaskiya, tare da bayyana aniyarsa ta ci gaba da ba da hadin kai domin a kammala binciken cikin nasara.