A yayin ci gaba da bincike, wani Mubarak Ladan, mai shekaru 28 daga Kamba, ya kai naira dubu ɗari shida (₦600,000) wa DPO Kamba, SP Bello Mohd Lawal, a matsayin cin hanci domin a saki wadanda aka kama. Shi ma an cafke shi tare da kuɗin a matsayin shaida.
Monday, 22 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

A yayin ci gaba da bincike, wani Mubarak Ladan, mai shekaru 28 daga Kamba, ya kai naira dubu ɗari shida (₦600,000) wa DPO Kamba, SP Bello Mohd Lawal, a matsayin cin hanci domin a saki wadanda aka kama. Shi ma an cafke shi tare da kuɗin a matsayin shaida.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya umurci Mataimakin Kwamishina na SCID, Birnin Kebbi, da ya ƙara ƙaimi wajen kamo sauran da suka tsere.

Ya jinjina wa DPO Kamba da ‘yan sa-kai bisa ƙwarewa da jarunta, tare da bukatar su ci gaba da irin wannan aiki don samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.

Kwamishinan ya kuma bukaci sauran DPOs su yi koyi da DPO Kamba, yana mai jaddada kudurin rundunar wajen murkushe duk wasu miyagu da ke aiki a kan iyakokin jihar.

Daga ƙarshe, ya roƙi al’ummar jihar da su ci gaba da ba ‘yan sanda da hukumomin tsaro haɗin kai don kawar da laifuka a jihar.