
Sojoji masu nagartacciyar lafiya na da muhimmanci sosai wajen tsaron Nijeriya, in ji Matawalle
Ministan ƙasa a ma’aikatar tsaron Nijeriya, Dr. Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana cewa ingantacciyar lafiyar dakarun sojoji na da alaka ta kut-da-kut da tsaron ƙasa.
Matawalle ya yi wannan bayani ne a Abuja ranar Talata, yayin bikin cika shekaru 20 da kaddamar da Shirin Lafiya na Ma’aikatar Tsaro (MODHIP) tare da haɗin gwiwar Cibiyar Binciken Sojojin Amurka (WRAIR Africa partnership).
“Soja mai koshin lafiya kuma mai kwarin gwiwa, shi ne mai mayar da hankali wajen kare kasarmu,” in ji ministan, a cewar sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar.
Ya yaba wa haɗin gwiwar MODHIP–WRAIR wanda aka fara tun a shekarar 2005, yana cewa hadin guiwar ya taka muhimmiyar rawa wajen kare lafiyar sojoji da fararen hula.
Shirin, wanda aka ƙirƙira tun farko don yaƙi da cutar kanjamau (HIV), yanzu ya faɗaɗa zuwa cibiyoyin kiwon lafiya na soja sama da 31 a fadin ƙasar. Ya zuwa yanzu shirin ya yi nasarar gwaji ga mutane sama da 560,000, ya dora kusan 400,000 kan magani na dindindin, ya horar da ma’aikatan lafiya sama da 18,000, tare da tallafa wa marayu da yara masu rauni 325 ta hanyar tallafin karatu da kuma koyon sana’o’i.
Matawalle ya jinjina wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa sanya harkar lafiya kan gaba cikin shirye-shiryen gwamnatinsa ta hanyar Health Sector Renewal Investment Initiative.
Haka kuma, ya gode wa Gwamnatin Amurka, PEPFAR, NACA, NCDC, NAFDAC da sauran abokan hulɗa bisa irin goyon bayan da suke bayarwa.
A jawabinsa, Darakta Janar na MODHIP, Birgediya Janar I.B. Solebo, ya bayyana cewa sama da kashi 80% na masu cin gajiyar shirin fararen hula ne, yana mai bayyana shirin a matsayin wata gada tsakanin tsarin kiwon lafiyar soja da na farar hula.
Shugaban Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yaba da wannan haɗin gwiwa, yana mai cewa samfurin haɗin kai ne da ya ceci rayuka a fadin ƙasar.
Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills Jr., ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa Nijeriya a fannin kiwon lafiya da tsaro.