Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shattima, a jawabinsa a Gaban dubban shuwagabannin duniya, ya bayyana manufar Najeriya akan kasar Palastinu.
Thursday, 25 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shattima, a jawabinsa a Gaban dubban shuwagabannin duniya, ya bayyana manufar Najeriya akan kasar Palastinu.

A cikin jawabin da aka watsa Najeriya ta jaddada goyon baya ga tsarin ƙasashe biyu tsakanin Falasɗinu da Isra’ila, tare da yin Allah wadai da tashin hankali a Gaza da Qatar.

Ta jaddada muhimmancin ɗabi’un ci gaba, juriya, da haɗin gwiwa a duniya domin magance rikice-rikice. Haka kuma, Najeriya ta nuna goyon baya ga gina dimokuraɗiyya a yankuna daban-daban na duniya.