Jihar kogi Ambaliyar ruwa ta shafe ƙauyuka da dama a jahar kogi
Thursday, 25 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Ambaliyar ruwa ta shafe kauyuka a Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta ce ambaliyar ruwa ta nutse ƙauyuka biyar a Ibaji, inda ta buɗe cibiyoyin ‘yan gudun hijira 42 don taimakon jama’a. Hukumar SEMA ta gano ƙauyuka 258 a cikin ƙananan hukumomi 8 da ke cikin haɗarin ambaliya. 

Ayau News ta ruwaito an fara yin feshi a sansanonin yan gudun hijira (IDP) don kare cututtuka, yayin da gwamnati ta shawarci mazauna bakin koguna su koma wurare masu aminci.