
Ana zargin matashi Mutawakkil, wanda aka fi sani da Tony, da kashe kakanninsa ta hanyar caka musu wuka a unguwar Kofar Ruwa da safiyar yau.
Rahotanni sun nuna cewa bayan kisan, matashin ya yi yunkurin tserewa ta shiga wani gida, amma al’ummar unguwar suka yi ƙoƙarin cafke shi. Daga bisani jami’an Hisbah na Dala suka iso wajen, suka mika lamarin ga ’yan sanda, waɗanda suka tabbatar da cafke shi tare da kai shi ofishinsu.
Kakannin nasa kuwa an garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu, sai dai daga bisani rundunar ’yan sanda ta Kano ta tabbatar da rasuwarsu.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce za a fitar da ƙarin bayani nan gaba.