Kwankwaso Ya Karyata Jita-Jitar Cewa Ya Mika Wasiƙar Neman Shiga Jam’iyya
Friday, 26 Sep 2025 00:00 am

Nagari Radio

Kwankwaso Ya Karyata Jita-Jitar Cewa Ya Mika Wasiƙar Neman Shiga Jam’iyya

Tsohon Gwamnan Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ya mika wasiƙar niyyar shiga wata sabuwar jam’iyya a ƙasar.

A wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya bayyana cewa ba su mika irin wannan wasiƙa ga kowace jam’iyya ba, yana mai jaddada cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Kwankwaso ya shawarci jama’a da su ci gaba da samun sahihan bayanai game da harkokinsa ta hanyar kafafen da aka tabbatar da sahihancinsu kawai.