
Wani jami’in ƴansanda a jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro.
Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar, da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro.
Rahotanni sun nuna cewa jami’in, wanda yake aiki a ofishin ƴansanda na Hotoro, ya shiga bayan gida ne lokacin da abin ya faru.
Wata majiya ta ce yayin da bindigarsa, ƙirar AK-47, ke rataye a wuyansa, sai ya matsa kunamar bindigar bisa kuskure.
“An samu bindigar, mai lambar rajista GT 4177, tare da harsashi ɗaya da aka harba. An lissafa harsashi 29 daga cikin 30 da aka ba shi”, in ji majiyar