
Yan fashi sun kashe mutane hudu, sun kuma sace tara a hare-haren da suka kai a jihar Neja
Aƙalla mutane hudu sun mutu kuma wasu tara aka sace lokacin da wasu da ake zargi ‘yan fashi ne suka mamaye garin Ibeto da wasu al’ummomi a ƙaramar hukumar Magama a jihar Neja
Mazauna garin sun gaya wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun mamaye garin a yammacin ranar Talata, suna shiga gida-gida suna harbe-harbe ba kakkautawa.