Ƴansanda Sun Fara Aiwatar Da Dokar Sanya Baƙin Gilashi Mota A jahohin Legas da Katsina
Friday, 03 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Ƴansanda Sun Fara Aiwatar Da Dokar Sanya Baƙin Gilashi Mota A jahohin Legas da Katsina 

Rundunar ƴansandan jihar Legas ta fara aiwatar da dokar da ta shafi amfani da gilashin mota mai duhu (tinted glass) a cikin jihar a ranar Alhamis. Wannan mataki na daga cikin shirin tabbatar da tsaro da bin ƙa’ida, tare da bin umarnin Sufeto Janar na ƴansanda, IGP Kayode Egbetokun.