
Gwamnan jihar Sokoto ya kai ziyarar jaje wajen al'ummar ƙananan hukumomin Sabon Birni da Isa da ke gabashin Sokoto domin jajanta musu kan hare-haren ƴanbindiga.
A ziyarar, gwamnan ya ba ƴangudun hijirar yankin naira miliyan 293 da buhun shinkafa 1,540 da sauran kayayyakin buƙata domin rage musu raɗaɗin da ma rage musu zafin zama a sansanin gudun hijira.
A ziyarar, Gwamna Ahmed Aliyu ya jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa, inda ya ce suna ƙoƙarin gaske domin magance matsalar.
A ƙaramar hukumar Isa, gwamnan ya ba iyalan mutum 65 da aka kashe naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, da kuma naira 250,000 da buhun shinkafa uku ga duk wanda ya ji rauni a harin.
Haka kuma gwamnan ya bayar da gudunmuwar naira miliyan 20 da buhun shinkafa 1,200 ga sansanin gudun hijira a yankin.
A ƙaramar hukumar Sabon Birni, Gwamna Aliyu ya ba iyalan waɗanda suka rasu guda 61 naira miliyan biyu da buhun shinkafa biyar, da kuma gudunmuwar naira miliyan 20 da buhun shinkafa 1,200 ga sansanin gudun hijira a yankin.
Gwamnan ya ce za su yi doka na musamman domin hukunci mai tsanani kan mau kwarmata bayanai ga ƴanbindiga, "masu kwarmata bayani ba su da gindin zama a jiharmu," in ji shi, kamar yadda mai magana a yawun gwamnan, Abubakar Bawa ya bayyana.
A game da tsaro, gwamnan ya ce sun ba jami'an tsaro motocin sintiri guda 180, sannan suna bayar da alawus ga dakarun da ke kan gaba wajen daƙile matsalar tsaro