
Jirgin Abuja–Kaduna ya koma aiki
Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta sake farfado da zirga-zirgar jirgin Abuja–Kaduna bayan wani lokaci da aka dakatar da shi bayan kifewar da yayi dauke da fasinjoji.
Daraktan hukumar, Dr. Kayode Opeifa, ya hau jirgin tare da fasinjoji domin tabbatar da ingancin sabis da tsaro. Ya ce za a kara kulawa da tsaro da jin dadin fasinjoji.