
Al’ummar wani yanki a Sokoto sun tura roko da neman alfarma ga gwamnati kan matsalar tsaro da ta ki ci ta ki cinyewa Mutanen sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta ba su damar ɗaukar makamai don kare kansu daga hare-haren ‘yan Lakurawa Shugaban su, Alhaji Adamu Kebbe, ya zargi gwamnati da sakaci da barin jama’a cikin halin kunci da matsi
Haka kuma, sun roƙi Gwamnatin Tarayya ta samar da tallafin kai tsaye ga ƙananan hukumomi domin su iya ɗaukar matakan gaggawa wajen kare jama’a daga hare-hare. Jihar Sokoto na daga cikin wuraren da rikicin ‘yan bindiga ya fi muni a shekarun baya-bayan nan, musamman a yankunan Isa, Sabon Birni, da Kebbe. Duk da cewa gwamnatin jiha ta amince da tsanantar barazana, mazauna na cewa matakan da ta ɗauka basu isa ba wajen tabbatar da tsaro.