
Wani tsohon jami’in sojin sama mai ritaya, Air Vice Marshal daga jihar Anambra, ya rasu a cikin jirgin British Airways da ke kan hanyarsa daga London zuwa Abuja a safiyar Litinin.
Jirgin, wanda ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Heathrow da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Lahadi, 5 ga Oktoba, ya kamata ya sauka a filin jirgin Nnamdi Azikiwe, Abuja, da misalin ƙarfe 5 na safe a yau Litinin.
Sai dai da tsakar dare, da misalin ƙarfe 1:30, matukin jirgin ya bayyana uzurin gaggawa da ya shafi lafiya inda aka gano marigayin ya rasu a cikin jirgin, lamarin da ya sa daga nan aka karkata akalar jirgin zuwa El Prat Airport da ke Barcelona, a kasar Spain.
Majiyoyi sun shaida wa wakilinmu cewa marigayin, wanda ake zaton yana da shekaru sama da 80, ya dade yana fama da rashin lafiya, kuma an fita da shi kasar waje ne daga Najeriya domin ci gaba da yi masa magani.
Kamfanin jirgin, British Airways, ya fitar da sanarwa yana bada hakuri ga fasinjoji, tare da tabbatar da cewa an tanadi wani jirgi domin su ci gaba da tafiyarsu zuwa Abuja.