Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar shugabancin INEC
Tuesday, 07 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar shugabancin  INEC

Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Yakubu, wanda aka nada a shekarar 2015, ya yi wa’adin shekaru biyar sau biyu a ofis.

A ranar Talata, ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche, kwamishina a hukumar, wacce za ta rike mukamin a matsayin mai rikon kwarya.

Tsohon shugaban hukumar ya roƙi tsofaffin abokan aikinsa da su ba wa mai rikon kwaryar cikakken hadin kai har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban hukuma na dindindin.

Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon shugaban hukumar zabe a kowanne lokaci daga yanzu.