
Tsaro: Shugaba Tinubu ya kira taron Majalisar Koli ta ƙasa da ta ‘Yan Sanda
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kira zama na musamman na Majalisar Koli ta Ƙasa (Council of State) da Majalisar ‘Yan Sanda (Police Council) domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da ke kara ta’azzara a sassan ƙasar nan da sauran manyan batutuwan ƙasa.
Taron, wanda za a gudanar a dakin taro na Majalisar Zartarwa a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, na nuna sabon ƙudurin Shugaba Tinubu na ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da dawo da kwarin gwiwar ‘yan kasa kan kokarin gwamnati wajen magance matsalar rashin tsaro.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Ofishin Harkokin Majalisar, Dakta Emanso Umobong, ya fitar a madadin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, an bayyana cewa an gayyaci mambobin majalisun biyu su halarci zaman ko dai kai tsaye ko ta yanar gizo.
Majalisar Koli ta Ƙasa, wacce Shugaban Ƙasa ke jagoranta, na kunshe da tsofaffin shugabanni, tsofaffin alkalai masu shari’a na ƙasa, gwamnoni da kuma Ministan Shari’a. Ita ce ke ba da shawarwari kan manyan manufofin gwamnati, musamman batutuwan tsaro da nadin mukamai.
Ita kuwa Majalisar ‘Yan Sanda, na da alhakin kula da yadda ake gudanar da ayyuka da tsarin shugabanci na Hukumar ‘Yan Sanda ta Ƙasa, ciki har da nadin manyan jami’ai da ladabtar da su.
Majiyar Fadar Shugaban Ƙasa ta shaida wa The PUNCH cewa tarurrukan za su yi nazari kan halin tsaro a ƙasar, su tantance cigaban da ake samu a harkokin soji da tsare-tsare, tare da fitar da sabbin matakai don dakile ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da rikice-rikicen ƙabilanci da ke addabar wasu jihohin Arewa da tsakiyar ƙasar.
Taron na Alhamis zai kuma haɗu da tattaunawa kan wasu muhimman batutuwan siyasa, ciki har da zaɓen wanda zai gaji shugaban hukumar INEC mai barin gado.
Taron Majalisar Koli na wannan makon zai kasance na biyu tun bayan hawan Tinubu mulki, kuma ana sa ran zai sanya sabon salo wajen haɗa kai tsakanin jihohi da tarayya don magance matsalolin tsaro da ke damun ƙasar.