Hukumomin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun sanar da matakin aurar da zawarawa da ƴanmata har 2,000
Saturday, 11 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Hukumomin jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun sanar da matakin aurar da zawarawa da ƴanmata har 2,000, shirin da gwamnati za ta ɗauki nauyi.

Hukumar Hisba ta jihar ce ta sanar da matakin inda ta ce an fara shirye-shiryen gudanar da ɗaurin auren bayan umarnin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

A baya, gwamnatin Kano ta sha aurar da dubban 'yan mata da zawarawa a ƙarƙashin wannan shiri da ake ganin ya samu tagomashi saboda matakai da sharuɗɗan da ake gindayawa.

A cewar hukumar Hisba, akwai ɗumbin mata da maza musamman zawarawa wadanda suke buƙatar yin aure amma saboda rashin sukuni lamarin ya ci tura, abin da ya sa gwamnatin Kano ta ware makudan kuɗaɗen don shirya gagarumin bikin aurar da su.

Mataimakin shugaban hukumar Hisba Dr Mujahid Aminuddeen ya ce tuni suka fara shirye-shiryen gudanar auren.

"Gwamna ne zai biya sadakin zawarawan da yanmatan da za a aurar," in ji shi.

Dr Mujahid ya ce matsin rayuwa ne ke hana mata da maza yin aure inda galibinsu ke gararanba a titi.

Ya ce namiji da macen da suke soyayya kuma suka gabatar da kansu da suke da niyyar aure ne, gwamnati za ta ɗauki nauyin hidimar aurensu ta hanyar biyan sadaki da kuma kayan ɗaki.

Sannan Hukumar Hisba ta ce za a shirya wa zawarawan da mazajen da za su aura lakca a kan muhimmancin zaman aure da kuma gudanar da gwajin cutuka don tabbatar da lafiyarsu.

Hukumar Hisbah ta ce ta ɓullo da wannan shiri ne don rage zawarawa da kyautata tarbiyyya a tsakanin al'ummar jihar.

A watan Oktoban 2023 an yi shagalin bikin auren zawarawa da 'yan mata 1,800 inda gwamnatin ta ba su kayan daki da jari.