An yi jana'izar Sojojin Najeriya 3 da 'yan bindiga suka kashe sakamakon harin da suka kai musu a jihar Kebbi.
Saturday, 11 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

An yi jana'izar Sojojin Najeriya 3 da 'yan bindiga suka kashe sakamakon harin da suka kai musu a jihar Kebbi.

Mai martaba Sarkin Zuru Alh Sanusi Mikailu Sami Sami Gomo III na daga cikin wadanda suka halarci jana'izar a babbar barikin sojoji dake Zuru ciki hadda mataimakin shugaban karamar hukumar Mulkin Zuru Hon Samaila Abdullahi da APC Chairman Zuru Alh Aliyu Abubakar Abiola 

A wata sanarwa da Abbakar Aleeyu Anache ya fitar ta bayyana cewa kafin rasuwar sojojin sun kai dauki ne a lokacin da suka samu labarin 'yan ta'addan sun kai wani hare tare da kokarin yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

Sojojin da suka rasa rayukansu sun kai dauki ne a dai-dai lokacin da yan bindigar suka kai hare-hare a wasu kauyukan kananan hukumomin Sakaba Danko-Wasagu da ke jihar Kebbi.

Abbakar Aleeyu Anache