
Soja Mai Muƙamin Kofur ya Kashe Kansa Bayan ya Kashe Matarsa a Barikin Neja
Wani mummunan lamari ya faru a sansanin sojoji na Wawa da ke Jihar Neja, inda wani soja mai suna Lance Corporal Akenleye Femi, da ke aiki a Bataliya ta 221, ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa.
Wannan abin bakin ciki ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025, lamarin da ya tayar da hankula a cikin sansanin, inda mazauna yankin suka shiga cikin firgici da mamaki.
Rahotanni daga rundunar sojojin Najeriya sun tabbatar da cewa an gano gawar sojan da matarsa a cikin gidansu da ke Block 15, ɗaki na 24, a wajen mazaunin sojoji masu ƙananan mukamai a sansanin.
Binciken farko ya nuna cewa Lance Corporal Femi yana bakin aiki a lokacin, sai dai ya nemi izini daga wajen manyansa domin zuwa gida don wani lamari na kashin kansa. Daga baya aka gano shi da matarsa sun mutu a ɗakinsu.
Hukumomin soja ta bakin Daraktan hulɗa da jama'a, Stephen Nwankwo sun tabbatar da cewa an adana gawar mamatan yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi don gano ainihin abin da ya jawo wannan mummunan lamari.
Rundunar Sojojin Najeriya ta bayyana alhinin ta kan wannan abin takaici, tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan, abokai da abokan aiki. Haka kuma ta yi addu’ar Allah Ya jikansu da rahama.
Kwamandan Runduna ta 22, Birgediya Janar Ezra Barkins, ya bayyana cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin, kuma sakamakon binciken zai kasance a fili ga jama’a.
Rundunar ta kuma nemi hadin kan jama’a da fahimtar su yayin da ake ci gaba da bincike, tare da tabbatar da cewa za a ɗauki matakan da suka dace domin kaucewa faruwar irin wannan abu a nan gaba.