Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata rahoton farmakin 'yan bindiga a kauyen Maku-ku
Monday, 13 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata rahoton farmakin 'yan bindiga a kauyen Maku-ku

Gwamnatin Jihar Kebbi ta karyata wani rahoto da daya daga cikin tashoshin rediyo na FM dake Birnin Kebbi ya watsa, wanda ya yi ikirarin cewa 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Maku-ku da ke Karamar Hukumar Sakaba tare da kashe mutane da dama.

Mai magana da yawun Gwamna, Ahmed Idris, ne ya fitar da wannan sanarwa a Birnin Kebbi a ranar Litinin, inda ya ce babu wani abu makamancin haka da ya faru a jihar Kebbi. Ya bayyana rahoton a matsayin yunkuri na bata sunan gwamnatin jihar.

Idris ya bayyana cewa harin da ake magana akai ya faru ne a Rijau, Jihar Neja, ba a Kebbi ba. Ya kara da cewa matakin kafa sansanin sojoji da Gwamna Nasir Idris ya dauka a Sakaba ya taimaka gaya wajen magance matsalar tsaro a yankin.

"Ina kira ga wannan tashar FM da ta janye rahotonta tare da ba da hakuri saboda yaudaran da ta yi wa jama’a.

"Ina kuma shawartar su da su dinga tabbatar da sahihancin rahotonsu kafin watsawa, domin batun tsaro batu ne mai matukar muhimmanci," inji shi.

Idris ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi da su yi watsi da rahoton tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, yana mai jaddada cewa labarin ba shi da tushe balle makama.