Rundunar Sojin Najeriya ta yi ƙarin Haske kan zargin yunƙurin juyin mulki
Sunday, 19 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

A cikin martaninsu na farko tun bayan yada labarin zargin yunƙurin juyin mulki a kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Hedikwatar Tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa soke wasu bukukuwa na bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai ba shi da alaƙa da zargin yunƙurin juyin mulki.

Ko da yake sanarwar ba ta karyata kai tsaye cewa wasu jami’an soja ba su da hannu a cikin zargin yunƙurin ba, ta ce binciken da ake yi kan jami’ai 16 da aka kama “tsari ne na cikin gida da ake gudanarwa akai-akai domin tabbatar da ladabi da ƙwarewa a cikin rundunar.”

Sojojin sun ce an kafa kwamitin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan jami’an da abin ya shafa, kuma “ Za a fidda komai a fili game da sakamakon binciken”.

PREMIUM TIMES ta buga cewa kimanin jami’an soja 20 aka kama bayan hukumomin tsaro sun samu bayanai kan zargin shirin juyin mulki. Rahotanni sun nuna cewa kama jami’an ya fara ne da mutum 16 a ƙarshen watan Satumba.

Sahara Reporters ce ta fara yada labarin zargin yunƙurin, kuma majiyoyin soja sun tabbatar wa jaridar cewa an kama jami’an ne bisa zargin wannan shiri.

A cikin sanarwar ta, DHQ ta mayar da hankali ne kan rahoton Sahara Reporters da ya ce an soke liyafar bikin ranar ‘yancin kai ta 1 ga Oktoba saboda wannan zargi.

A cewar sanarwar, an soke bikin ne “domin bai wa Shugaba Tinubu damar halartar muhimmin taron ƙasa da ƙasa a waje, da kuma bai wa sojoji damar ci gaba da ƙoƙarinsu wajen yaƙar ta’addanci, da sauransu.

“Rundunar Sojojin Najeriya na son ta fayyace cewa dukkan zarge-zargen da wannan kafar yada labarai ta yi ƙarya ne kuma na son tada hankali,” in ji sanarwar.
“Soke bikin yana da dalilai na gudanarwa kawai, ba shi da alaƙa da wani yunƙurin juyin mulki.”

DHQ ta roƙi ‘yan Najeriya su yi watsi da abin da ta kira “ƙarya da makiyan ƙasa ke yadawa,” tare da sake jaddada biyayyarta ga Kundin Tsarin Mulki da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.