Yaƙi da Rashin Tsaro Wajibi Ne Na Kowa: Inji Gwamna Lawal
Monday, 20 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Yaƙi da Rashin Tsaro Wajibi Ne Na Kowa: Inji Gwamna Lawal

Gwamna Dauda Lawal ya tunatar da dukkan masu ruwa da tsaki cewa, yaƙi da matsalar rashin tsaro a Jihar Zamfara wajibi ne da ya rataya a wuyan kowa a cikin gwamnatinsa.

A ranar Litinin, gwamnan ne ya jagoranci taron majalisar zartarwa na 18 a gidan gwamnati da ke Gusau.

A taron, majalisar ta tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi tsaro, ilimi, lafiya, da ci gaban gine-gine da sauransu.

A cikin jawabin sa na bude taro, gwamna Lawal ya ce, “Ina so in tunatar da mu duka game da nauyin da ya rataya a wuyanmu a cikin wannan gwamnati dangane da yaƙi da rashin tsaro.

“Mun samu ci gaba mai yawa, inda muka samu nasarar dawo da zaman lafiya a yawancin yankuna na jihar. An takaita ta’addancin ’yan bindiga, sabanin yadda abin yake a shekarun baya.”

Ya ƙara da cewa, “Ina roƙonku da ku kasance masu faɗa a ji, ku kasance kusa da jama’ar yankunku da kuma jami’an da aka zaɓa a kananan hukumomi, tare da ci gaba da bayar da rahotannin halin da ake ciki ga kwamishinan tsaro. Mu yi addu’a ga rayukan jarumanmu da suka rasu.”

Gwamna Lawal ya kuma ƙarfafa wa mambobin majalisar guiwa su ƙara haɗin kai da sauran jami’an gwamnati da na siyasa domin tabbatar da ingantacciyar aiki tare da cigaban jihar.