Budurwa ta kashe kanta saboda auren dole a jihar Borno
Monday, 20 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Budurwa ta kashe kanta saboda auren dole a jihar Borno

Wata matashiya ta halaka kanta a ƙaramar hukumar Gubio da ke jihar Borno, bayan da mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.

Rahoton da shafin Zagazola Makama ya wallafa ya nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi da misalin ƙarfe 6:20 na yamma. Majiyoyi sun bayyana cewa marigayiyar ta sha matsin lamba daga iyayenta domin ta amince da auren da aka shirya mata, duk da cewa zuciyarta tana son wani saurayi daban.

Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Bukar Fantami Gubio, ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce damuwa da matsin lambar da ta fuskanta daga gida ne suka jawo ta yanke shawarar kashe kanta.

Ya bukaci hukumomin kare haƙƙin ɗan adam da jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar matakan da za su hana maimaituwar irin wannan auren dole a nan gaba.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ‘yan sanda da gwamnatin jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma kan lamarin ba.