
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci alƙalai da sauran ma'aikatan ɓangaren shari'ar ƙasar da su ƙara ƙaimi, tare da yin aiki na ‘ba sani-ba sabo’ wajen tabbatar da adalci.
Tinubu ya bayyana haka ne a taron ƙara wa juna sani ga alƙalai da Hukumar EFCC tare da haɗin-gwiwar hukumar shari'a ta Najeriya suka shirya a Abuja.
Shugaban ya yi gargaɗin cewa ana fara samun matsala ne a ƙasa da zarar waɗanda aka ba amanar tabbatar da hukunci sun fara cin amana da tauye haƙƙin mai haƙƙi.
Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu, ya ce gwamnatinsu ba ta sa baki a harkokin shari'a, tana mai cewa: "mun ba ɓangaren shari'a da hukumomin yaƙi da cin-hanci damar gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba".
Da yake bayyana irin nasarar da suka samu wajen yaƙi da cin-hanci da rashawa, Shettima ya ce EFCC ta samu nasarar ƙwato dukiya da ta haura Naira biliyan 500 a cikin shekara biyu.