
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bai wa wata matashiya mai suna Joy Ogah damar zama a kujerarsa na mataimakin shugaban ƙasa na tsawon rana guda.
Lamarin ya faru ne a Fadar shugaban ƙasa lokacin da Shettima ya karɓi tawagar PLAN International, ƙarƙashin jagorancin shugabar ƙungiyar, Helen Mfonobong Idiong.
A yayin taron, Shettima ya jaddada aniyar gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ƙara inganta ilimin ‘ya’ya mata a faɗin ƙasar.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da yin aiki tare da PLAN International domin tabbatar da cewa shawarwarin da ƙungiyar ta bayar kan ilimin yara mata sun samu karɓuwa da kuma aiwatarwa yadda ya kamata.
Mataimakin shugaban ƙasan ya kuma bayyana cewa ci gaban ‘ya’ya mata muhimmin ginshiƙi ne wajen gina ingantacciyar ƙasa.
A nata ɓangaren, matashiyar Joy Ogah ta nuna farin ciki da godiya bisa wannan dama, inda ta ce mata na da ƙwarewa da basira wajen jagoranci, musamman idan hukumomi da masu ruwa-da-tsaki suka samar musu da damar da ta dace.