Shugaban Kungiyar nan dake fafutukar ballewa Daga Najeriya IPOB NNamdi Kanu ya ambato sunayen wasu muhimman mutane a cikin kasa da suka hada da Tsohon Ministan Shari'a Na kasa Abubakar Cika Malami da kuma Ministan Birnin tarayya Abuja Nyesom wike kana da
Wednesday, 22 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Shugaban Kungiyar nan dake fafutukar ballewa Daga Najeriya IPOB NNamdi Kanu ya ambato sunayen wasu muhimman mutane a cikin kasa da suka hada da Tsohon Ministan Shari'a Na kasa Abubakar Cika Malami da kuma Ministan Birnin tarayya Abuja Nyesom wike kana da gwamnan Jahar Lagos Babjide Sanwo Olu da Sauran su a matsayin shedu.

Yayin da yake kokarin Gabatar da shedu Kan tuhume tuhumen Ta'addancin da Ake zargin Shi dasu, Kanu ya ambato sunayen muhimman mutanen ne a matsayin Wadanda suke shedun sa.


Wannan na kunshe ne a cikin wata sabuwar bukatar da ya Gabatar wa mai Shari'a justice James Omotosho Wanda ya sanyawa hannu a jiya a wani mataki na Gabatarwa kotun shedun sa don wanke kanshi Daga zarge zargen da Ake mishi.

Yayin Gabatar da shedun, Kanu Ya Kuduri aniyar Gabatar da Akalla shedu 23 Wadanda ya kasafa gida biyu, inda ya bukaci kotun ta bashi Kwanaki 90 domin kammala tattara shedun Shi.