Babban Ministan Shari’a na Najeriya kuma Babban Lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi (SAN), ya umarci wasu hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan jerin sunayen mutanen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa,
Thursday, 23 Oct 2025 00:00 am

Nagari Radio

Babban Ministan Shari’a na Najeriya kuma Babban Lauyan Gwamnati, Lateef Fagbemi (SAN), ya umarci wasu hukumomi su gudanar da cikakken bincike kan jerin sunayen mutanen da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa afuwa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumomin da za su gudanar da wannan bincike sun haɗa da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), da kuma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa binciken na iya kaiwa ga cire fiye da rabin sunayen waɗanda aka saka cikin jerin masu cin gajiyar afuwar.

A halin yanzu, Shugaba Bola Tinubu na jiran a mika masa jerin sunayen da aka tantance domin ya sanya hannu na ƙarshe, a wani mataki na tabbatar da cewa duk wanda zai amfana daga afuwar ya cancanta sosai.

Tun da farko, Tinubu ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ba shi wajen yi wa mutum 175 da aka samu da laifuka daban-daban afuwa.

Minista Fagbemi ne ya bayyana hakan yayin taron Majalisar Mahukunta da aka gudanar a ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025.